Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Jihar kaduna ta tabbatar da samun karin mutum daya da ya kamu da cutar korona, abin da ya kawo jumillar adadin wadanda suka harbu da ita a jihar zuwa 10.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, gwamnatin ta ce mutumin da ya kamun ya yi mu’amala ne da daya daga cikin wadanda suka kamu a farkon wannan makon.
Ya zuwa yanzu Kaduna ta sallami mutum shida da suka warke, ciki har da Gwamna Nasir El-Rufai, wanda aka sallama ranar 22 ga watan Afrilu.
Ta ce hukumar NCDC ta kafa cibiyar yin gwajin cutar a boirnin Kaduna kuma tuni aka gwada mutum 133, yayin da ake kan tantance wasu cibiyoyin biyu a Zaria da Kaduna.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *