Adadin mutanen da suka kamu da cutar korona ya kai tara a jihar Kano da ke arewacin Najeriya bayan an sanar da karin mutum biyar da suka harbu da cutar ranar Laraba.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma’aikatar lafiyar jihar ta ce ya zuwa karfe 10:25 na safiyar Laraba, “adadin masu dauke da cutar a Kano ya kai tara.”
A ranar Asabar ne hukumomi suka sanar da manema labarai cewar wani mutum ya kasance na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.
Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda yake zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajibirin ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.
Gwamnatin jihar ta Kano ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumin ya kai ziyara kafin a gano yana dauke da cutar.