
Adadin mutanen da suka kamu da cutar korona kawo yanzu ya kai 27 a Kano, bayan da aka sanar da karin mutum 6 da suka harbu da cutar a daren Juma’a.
Kano dai a yanzu ita ce ta uku wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya, baya ga Legas da Abuja, kuma har ma ta yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Laraba.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma’aikatar lafiyar jihar ta ce ya zuwa karfe 10:56 na daren Juma’a, “adadin masu dauke da cutar a Kano ya kai 27, sannan mutum 1 ya mutu.”
Wannan adadi na zuwa ne kasa da mako guda da samun bular cutar karo na farko a Jihar.
A wannan juma’ar aka sanar da cewa shugaban kwamitin da ke yaki da cutar a Kano ya kamu da cutar kamar yadda ma’aikatar lafiyar jihar ta sanar.
A ranar Asabar ne kuma hukumomi suka sanar da manema labarai cewar wani mutum ya kasance na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.
Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda yake zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajibirin ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.
Gwamnatin jihar ta Kano ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumin ya kai ziyara kafin a gano yana dauke da cuta