Shugaban Kungiyar kwallon kafa ta kano pillars dake kano a Najeriya Alhaji Surajo Shaaibu Yahaya Jambul yace kungiyar kano pillars na sane da irin karfin da kungiyar ASC Jarraf ta Senegal ke dashi,
A wata tattaunawa da wakilinmu surajo jambul yabayyana kungiyar. ta kasar Senegal .da cewa kungiya ce da tarihi ya nuna tafi karfi wasan da take bugawa a waje, abin da Jambul din ke cewa hakan nada ban tsoro kwarai,
Yayin da Jambul din ke cewa kungiyarmu ta Kano Pillars a shirye muke dan tunkarar kowane irin kalu bale cikin yardar Allah kuma irin adduoin da magoya bayanmu ke yi mana muna fatan Allah zai amsa ya bamu Sa’a.
Da yake amsa tambaya kan yadda kungiyar take tun bayan sauyin maihoraswa shugaban cewa yayi kawo iyanzu komai na tafiya kamar yadda ya kamata kuma yanwasan na bada goyon bayan da ake bukata, kan kalubalen dake gaban kungiyar na rashin wasa a gida kuma ba tare da yan kallo ba,surajo jambul cewa yayi babu dadi kuma indan sammune to muyi wasa a gida amma wasu dalilai sun sanya dole muje wata jihar, to ya zama dole ga yan wasanmu su dage don ganin sun baiwa mara Da kunya a dukkan wasannin mu,
Tuni kungiyar Kano Pillars ta bar Kano Zuwa Jihar Kaduna inda zata cigaba da daukar horo kafin tashinta zuwa kasar Senegal