Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban karamar hukumar Tarauni Abubakar Zakari Habu P.A ya jaddada aniyarsa na yin aiki kafada kafada da ofishin hakimin Tarauni sarkin fadar kano,

Habu P.A ya bayyana haka ayayin daya karbi bakuncin Hakimin Tarauni sarkin fadar kano da duk dagatai da masu unguwannin na karamar hukumar.a ofishinsa, Habu P.A wanda ya nuna jin dadinsa da ziyarar da yace iyayensa sun kawo masa ya shaalwashin bawa ofishin hakimin cikakken goyon baya dan ganin an ciyar da karamar hukumar gaba,

Da yake jawabi hakimin Tarauni sarkin fadar kano Malam Ado Kurawa ya godewa shugaban karamar hukumar bisa kyakykyawar tarba da akayi masa da daukacin tawagarsa inda yace sunzo ofishin shugaban karamar hukumar ne dan tayashi murnar zama shugaban karamar hukumar tare da jadada goyon bayansa ga sabon shugabancin da hakimin yace na matashine wanda ya goge da hulda da jama’a, inda ya adduar Allah yayi masu jagorancin,

A wani labarin shugaban karamar hukumar Habu Zakari ya amince da karin kaso dari da alawus da ake bawa kungiyar Vigilante ta yankin karamar hukumar sakamakon koke da yan kungiyar suka kai masa yayin wata ziyara da sukai masa ranar laraba a ofishinsa,

Habu Zakari Habu P A yace amincewa da karin ya zama wajibi laakari da yadda yan kungiyar ke bada lokacin su da rayuwar su da kare rayuwar alummar yankin,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *