Kyaftin din Manchester United Harry Maguire ya yi imanin cewa kungiyar ta samu ci gaba a kokarin shiga jerin kungiyoyi hudu na saman teburi, bayanda ta gaza samun maki uku a hannu Southampton a daren Litinin.
Kungiyar Ole Gunnar Solskjaer ta yi kokarin rike nasarar da ta samu tare da cin nasara a zura kwallaye 2 da 1 akan Southampton a Old Trafford amma Michael Obafemi ya farke kwallo bayan bugo kwallo daga kusurwa.
Southampton ce ta fara zura kwallon ta hannun Stuart Armstrong a minti na 12 kafin cin kwallaye daga Marcus Rashford da Anthony Martial suka sa United kan gaba sai dai Obafemi ya farke kwallon a minti na 96.
“Mun inganta kan kare hare-hare aa wasannin da muka sanya gaba,” Maguire ya fada wa Sky Sports. “Mun fara da mummunan sakamakon kakar amma yanzu mun kokari samun nasarori a mafi yawan wasanni.