CMShugaban kungiyar kwallon kafa ta Dandidi Babes dake garin Gumel a jihar Jigawa Najeriya Alhaji Bashir Dandidi yace lokaci yayi da masu hannu da shuni zasu sanya jari kan harkokin wasannin matasa,
A wata tattaunawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja jin kadan bayan kammala wata ziyara daya kai ofishin hukumar wasan kwallon kafa ta kasa NFF, Bashir Dandidi ya bayyana dalilansa na kafa kungiyar wasan kwallo da suka hadar da tallafawa matasa kan bkatunsu na harkokin motsa Jiki, Hada kawunan matasa dan samar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikinsu, kauda Matasa da Ayyukan Ashsha da karesu daga ta’ammali da shan miyagun kwayoyi, da tallafa musu kan harkokin karatunsu,
Dandidi ya kara da cewa kawo iyanzu kungiyarsa ta sami nasarar data zama abin alfahari ga masarautar da jihar Jigawa baki daya, inda kungoyar ta fara daga rukunin ajin matasa na uku zuwa na biyu har zuwa na daya wanda kungiyar ke ciki a halin yanzu,
Da yake karin haske kan halin da matasan ke ciki a garin Gumel sakamakon kirkirar kungiyar Dandidi Babes shugaban kungiyar cewa yayi yanzu mstasa sun sami abinyi kuma an dauke hankalinsu daga wasu tunani marasa kyau inda kara da cewa ba matasan dake wasan kawai kungiyar ta taimaka ba har matasa masu kallo da manya da yara mata da maza da kan je filin atisaye da lokacin wasa inda suke baje kolin kasuwanci kananan sanaoi da sukanyi lokacin da ake wasanni,