Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kwanaki biyu bayan da motar kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta kama da wuta sa gashi a ranar jumaa Motar dake dauke da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta kama da wuta akan hanyarta ta zuwa Makurdin jihar Benue don yin wasanta na mako na 11 kungoyar kwallon kafa ta Lobi Stars.

Rahotanni sun ruwaito cewa motar dake dauke da ‘yan wasan ta kama da wuta ne a dai-dai karamar hukumar Doguwa.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe sha daya da mintuna arba’in na safiyar ranar Juma’a.

Sai dai babu wanda ya rasa ransa ko ya ssamu rauni mai magana da yawun kungiyar Lurwani Idris Malikawa yace matsalar ba wacce zata tada hankali bace sabanin wasu rahotanni dake munana abin inda yace motar hayaki ta fara a lokacin da yan wasa kecin abinci a unguwar Bawa inda malikawa yace tuni motar ta dawo Kano yayin da aka saka yan wasan a wata motar dan isa grain Makodi inda zasu bugs wasan mako na 11 da kungiyar Lobi Stars

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *