Duk da yana yin far gaban da wasu kasahen Duniya ke ciki game da cutar COVID-19 amma miliyoyin musulmi sun gabatar da sallar juma’a a yau a jihar Kano.
Duk inda ta kazagaya a jihar Kano zakatar da dimbin alumma sun halarci salla a yau.
Ya yin da kasashe irin su Iran suka dakatar da yin Sallar juma’a a tare dan gujewa bazuwar cutar.
Tuni dai gwamnatin Kano a wani yun kuri na kare kai ta samar da jami’an Lafiya da zasu rika gwada ma’aikatan fadar gwamnatin Kano da sauran baki.
Zuwa yanzu dai rahoton mutum daya aka samu dan asalin kasar Italiya wanda ya shigo cikin Najeriya dauke da cutar wanda aka killaceshi a cibiya ta musamman dake Legas.