Allah ya yi wa mawallafin Jaridar Leadership, Mista Sam Nda-Isiah rasuwa yana da shekaru 58 a duniya.
Majiyoyi sun bayyana wa The Nation cewa marigayin ya rasu misalin ƙarfe 10 na daren ranar Juma’a bayan ya koka kan cewa baya jin daɗin jikinsa.
Nda-Isiah ya hallarci taron kungiyar masu jaridu ta Najeriya, NPAN, a jihar Legas a ƙarshen mako.
Marigayin wanda haifaffen jihar Niger ne ya yi karatun digiri a fannin kimiyyar magunguna a Jami’ar Ife.
Ya kuma taɓa neman tikitin takarar kujerar shugabancin ƙasa a jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Wani daga cikin iyalansa ya shaidawa wakilin jaridar Punch a wayar tarho cewa:
“Eh, da gaske ne. Yanzu aka sanar dashi ‘
Sai dai wasu daga cikin fitattun mutane ciki har da kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi ta’aziyar rasuwarsa.
An haife shi a shekarar 1962 a Minna, Jihar Niger. Mista Nda Isaiah kuma yana da sarautar Kakakin Nupe a jihar Niger.