Kwamitin zartarwar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya zai gudanar da taro a Alhamis ɗin nan, kwana guda bayan sabon shugaban jam’iyyar na riƙo ya samu tabarrakin Shugaba Muhammadu Buhari.
A jiya ne bbc tace Muhammadu Buhari ya bayyana amincewa da mataimakin sakataren APC na ƙasa, da aka dakatar, Victor Giadom a matsayin halattaccen shugaban riƙon jam’iyyar.
Masharhanta a Najeriya irinsu Dr. Abubakar Kari sun bayyana matakin a matsayin mai cike da ban mamaki da kuma ɗaure kai. Don kuwa a cewarsa: “sanarwar, wani babban al’amari ne kuma tasirin da za ta iya yi yana da girman gaske”.
Ya ce hakan na nufin sai dai su Bola Ahmed Tinubu wato jagoran APC na ƙasa da kuma ɓangaren Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar da aka dakatar, su je su sake shiri.
“Ko dai su je su sake zawarcin Buhari don ya sabunta musu goyon baya, ko kuma su san yadda za su yi,” in ji masanin kimiyyar siyasa na Najeriya.
Wannan mataki na Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya yi hannun riga da matsayar zaɓaɓɓun shugabannin APC da suka tabbatar da mubaya’arsu ga Sanata Abiola Ajimobi.
Shi ne dai mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar kudu maso yamma, kuma a cewar shugabannin APC, sun ɗauki matakin ne bisa la’akari da tanadin tsarin mulkin jam’iyyarsu.
Sai dai wata sanarwar fadar shugaban Najeriyar ta bayyana inkari kan matsayin shugabannin jam’iyyar tun da farko, inda ta ce Shugaba Buhari ya yi imani cewa Victor Giadom ne halastaccen shugaban riko.
Sanarwar ta ce shugaban ya kafa hujjar wannan mataki da ya ɗauka bayan shawarwarin masana shari’ah da ya samu a kan halin da jam’iyyarsu ta APC ke ciki.
Har ma Shugaba Buhari ya bayyana aniyar halartar taron da Victor Giadom ya kira ranar Alhamis, wanda za a yi ta bidiyo, kuma ana sa ran cewa gwamnoni da shugabannin majalisar dokoki na APC za su halarci taron.
Dr. Abubakar Kari ya ce a ganinsa matakin, babbar koma-baya ce ga ɓangaren Adams Oshiomhole da kuma Asiwaju Ahmed Tinubu waɗanda da ma su ne ake ta jayayya da su a kan shugabancin APC.
“Kuma bai yi daidai da irin halin Buhari da aka sani na rashin tsoma baki da nuna halin ko’in kula, idan ana rigima a cikin jam’iyyarsa ba,” in ji shi.