Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kwamishnan matasa da wasanni na jihar kano kwamared Kabiru Ado Lakwaya yace tabbas jihar kano zataci gaba da rike matsayinta na jagaba a fagen wasannin kwallon kafa a yakin arewa maso yamma da arewacin Najeriya baki daya duba da yadda take sanar da matasan yan wasa,

A tattaunawarsa da wakilinmu Salisu Musa Jegus jin kadan bayan kammala wasan karshe na cin kofin APC UNITY CUP da kungiyar samarin Jamiyyar na shiyyar Arewa Maso Yamma ta shirya a jihar kano yace abin daya gani kuma duniya ta sheda wani abune da yake alamta irin yadda matasan kano ke tasowa a fagen wasan kwallon kafa,

Dan gane da yadda gwamnatin Jihar ke tallafawa harkokin matasa da wasanni Lakwaya cewa yayi ” Gwamna Ganduje yayi zarra wajen kula da matasa ko nima kai amsace kan irin yadda gwamnan ke son matasan jihar kano” dubi maaikata sukutum da guda dubi kwamishinan daga cikin matasa ko Kano Pillars Matashi ke Jagorantarta ai mu matasa sai godiya ga gwamna Ganduje,

Kan Nasarar da mstasan yan wasan suka samu a wasan karshen kan takwarorinsu na Jihar Kebbi Kwamared Kabiru Lakwaya cewa yayi yaran kano sunyi kokari idan ka dubi yadda yan wasan Kebbi ke da girma da karfin jiki, wannan nasarar ita take Nuna irin kyakykyawar makomar da matasan namu ke dashi nan da shekaru masu zuwa,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *