Gamayyar ƙungiyoyin matasan arewacin Najeriya ta bayyana takaici game da taron gwamnoni da sarakuna da sauran manyan jagororin yankin suka yi a Kaduna.
Bbc taruwaito matasan na ganin taron ya yi wasarairai da manyan matsalolin da ke addabar al’ummar yankin kamar tashin-tashinar matasa da rashin aikin yi, inda ya ɓuge da zanga-zangar EndSARS da kuma ƙorafi kan shafukan sada zumunta.
A cewarsu taron ya gaza wajen yin ta-maza ya fayyace matsayinsa kan hare-haren da aka kai wa ‘yan arewa waɗanda ba su ji, ba su gani ba a wasu yankunan kudanci.
Ɗaya daga cikin jagororin matasan, Nastura Ashir Shariff, ya shaidawa BBC cewa abin takaici ne ace jagororin kudancin Najeriya na kwatowa al’ummar yankinsu haƙƙinsu, amma lamarin ba haka yake ba a Arewa.