Matar shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari, ta ce labarin da take samu game da yawaitar yi wa mata fyade yana matukar tayar mata da hankali.
A sakon da ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Twitter, Aisha Buhari ta ce: “Abin tayar da hankali ne samun labarin kisan da ake yi wa ‘ya’yanmu mata, wadanda maza suke yi wa fyade na rashin imani; wasu lokutan ma iyayensu da ‘yan uwansu da kuma masu kula da su ne suke yin hakan.”
Matsalar fyade dai tana neman zama ruwan dare a Najeriya, inda a baya bayan nan aka samun labarin yi wa wasu mata fyade a sassa daban-daban na kasar.
Daya daga cikinsu ita ce wata yarinya mai shekara 12 wacce ta shaida wa ‘yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.
Kazalika, a makon jiya an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami’a bayan sun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.
Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.
Contact Information
114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano
We Are Available 24/ 7. Call Now.
- 22 September, 2023
Share: