Mataimakin gwamnan jihar Benue, Benson Abounu, ya shawarci mahukuntan jihar Ondo, Oyo da sauran jihohin da ke fama da rikicin makiyaya a kasar nan da su yi la’akari da kafa dokar hana kiwo a fili irin na jihar Benue, The Punch ta ruwaito.
Jihohin Oyo da Ondo sun kasance cikin guguwar kwanan nan dangane da kalubalen tsaro da kuma kokarin kula da zirga-zirgar makiyaya.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce jihar ta kafa dokar hana kiwo a fili amma ya ce akwai kalubale wajen aiwatar da dokar.
Gwamnan ya kara da cewa hadin kan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na tarayya na da matukar mahimmanci wajen aiwatar da dokar da aka kafa domin dakatar da yawan rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Dokar da mataimakin gwamnan Benue ya ce na aiki sosai a jihar. Inda Ya yaba wa rundunar ‘yan sanda ta Jihar Benuwai kan jajircewa da sukayi dan aiwatar da dokar hana kiwo a fili a jihar.
Ya kuma ce gwamnatin jihar ta kame shanu 356 da makiyaya shida dauke da makamai kwanan nan kuma an mikasu da shanunsu ga ‘yan sanda don gurfanar da su.
.
“Adadin da yawa (na masu laifi) an kama su a baya kuma an yi musu shari’a daidai da laifinsu. Wasu daga cikinsu an yanke musu hukunci a cibiyoyin gyara yayin da wasu suka biya tara.”
Mataimakin gwamnan ya kuma lura cewa gwamnatin jihar ba ta adawa da kiwon shanu, ya kara da cewa a koyaushe tana ba makiyaya a jihar sha