Daga-Zaharadden Abdullahi Bichi
Tashar Radio Express tana a matsayin jigo wajen tallafawa cigaban ilimin mata a fadin jihar kano.
Bayanin hakan ya fito tab akin Malama Najibat Kabir Yahaya yayin ziyarar da suka kawo gidan rediyon Express a yau.
Malama Najibat, tace ilimin mata yana da matukar amfani wajen cigaban rayuwar al’umma, tana mai cewar Express rediyo na guda daga kafafan dake taimakawa wajen bunkasar ilimin ‘ya’ya mata. -Editor Aisha A. Isma’il
