Iyaye mata a jihar Edo na gudanar da zanga-zanga inda suke kira gwamnati ta kori Fulani Makiyaya daga jihar.
Matan sun tare hanyoyi a Uromi, karamar hukumar Esan ta jihar.
Rike da takardu masu rubutun #FulanimustGo, matan sun ce zuwa gonakinsu ya gagara saboda suna tsoron kada makiyaya su kashesu.