Shekaru 100 bayan dokar da da ta ba mata ‘yancin yin zabe, mata masu kada kuri’a na tasiri sossai a zabukan Amurka.
A duk zabukan shugaban kasa na Amurka da aka yi tun daga shekarar 1964, an samu karin mata fiye da maza da suka kada kuri’a kuma tun daga shekarar 1980, jinsunan biyu sun sha bamban sosai a ra’yoyinsu na kada kuri’a.
Wata ‘yar Najeriya ce da ke zama a jihar California a Amurka, ta ce mata na taka muhimmiyar rawa sosai a zabukan kasar tun bayan da suka samu yancin kada kuri’a.
Ta ce…. “mata bakar fata musamman masu ruwa da tsaki a jami’iyyar Democrat sune ke karfafa gwiwar mata ‘yan uwansu da ma sauran jama’a akan su fita yin zabe.”
Voa ta ruwaito wani binciken jaridar Bloomberg ya nuna cewa mata sun fi maza zaben ‘yan takara daga jam’iyyar Democrat, musamman ma an fi ganin bambancin ra’ayin a lokacin gwamnatin shugaba Donald Trump.
A nasarar ban mamakin da ya samu a zaben shekarar 2016 lokacin da ya kara da Hillary Clinton, mace ta farko da ta tsaya takarar Shugban kasa a jam’iyyar Democrat, Trump ya samu kuri’un maza kashi 52 cikin 100 mata kuma kashi 41. Wannan gibin na kashi 11 shine mafi yawa da aka taba samu a tarihin zaben shugaban kasa cikin karni 4 da suka gabata.
Dangane kuma da abinda ya sa mata da maza su ke da bambancin ra’ayi, a zaben yan takara, da kuma abinda hakan ya ke nufi sai Helen Bako ta bayyhana cewa,….. “Yawanci lokuta jam’iyyar Democrat ta fi ba mata zarafi su tsaya takara ba kamar jam’iyyar Republican ba. Ta kuma ce a zaben na bana mata da yawa sun fita kada kuri’a, musamman mata matasa.”