Dubban ‘yan Israi’la sun gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv, don nuna adawa da abin da suka kira kangin tattalin arziki da salon gwamnati na yaki da annobar korona ya tsunduma al’umma ciki.
Matasa da dama sun cika maƙil a dandalin taro na Robin Square sanye da takunkumai, sai dai ba tare da bayar da tazara ba.
A birnin Kudus kuwa daruruwan mutane sun taru a kofar gidan Fira minista Benjamin Netanyahu, suna kiran ya sauka daga kan kujerarsa.
‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi, domin tarwatsa dubunnan masu zanga-zangar, abin da ya rikide ya koma tashin hankali.