Daga-Abubakar Sale Yakub
Wasu masu sana’ar wani da guga dake nan Jihar Kano sunce, duk da kokarin da suke wajen farantawa abokan harkokin su rai amma su basa tausaya musu.
Sun shedawa Tashar Radio Express Radio, cewa “mutum sai ya kawo maka kaya guda goma amma ba zai iya cirar rabin kudin ya baka ba” a cewar su.
Wasu kuma idan aka samu tsautsayi na konewar kaya to fa saika biyasu, wanda kamata yayi ace suna biyan kudaden tamkar yadda suke musu wahala.
Duk da wadan nan tarin matsaloli da suke fusakanta amma sunce suna samun abin da zasu ci su kuma kaiwa iyalansu da ‘yansu a garuruwansu.