Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 62,691 bayan da aka gano ƙarin mutum 170 da suka kamu da cutar ranar Jumma’a.
Adadin mutum 58,430 sun warke kuma an salleme su, yayin da 1,144 suka kwanta dama zuwa yanzu.
Jihar Legas ita ce mai adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu a ranar Jumma’a, da mutum 106, Sai Abuja mai mutum 25 da suka kamu.
Oyo na da mutum 14, Edo da Kaduna kuwa na da mutum 7-7 da suka kamu da koronar a kowacce jiha.
Ogun ta samu mutum 4 da suka kamu, sai Bauchi da Benue masu mutum 2-2.
Jihohin Kano da Osun da kuma Rivers na da mutum dai-dai da suka kamu a kowacce jiha.