Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

,

Wasanni na taka mahimmiyar rawa wajen hada kai, samar da zaman lafiya, da bunkasar tattalin arziki a kasashen da suka ci gaba, ko a kasarmu Najeriya anyi Ittifaki wasanni na daya daga cikin abin dake sanya yan kasar zama inuwa daya ba tare da banbancin Yare, Kabila ko Addini ba,

A wata tattaunawa da Express Radio tayi da Dan Isan Katsina Hakimin Rimaye Alhaji Yusuf Yakubu kuma shugaban Hukumar kwallon Fives na Jihar cewa yayi tabbas wasanni na taka rawa wajen cigaban alumma a matakai daban daban kama daga Hadin kai, Zaman Lafiya, Hana Shaye Shaye, da samar da Sana’a, da yake amsa tambaya kan irin rawar da masarautu ke takawa wajen cigaban wasannin tsakanin matasa, Dan Isan Katsinan cewa yayi Masarautu suke kan gaba waje kulawa da abin da matasa keda bukata duba da cewa sune manyan gobe, dayake bada misali Dan Isa cewa yayi kawo iyanzu a masarautar Rimaye dake katsina inda yake iko yace matasa na anfana da irin tsarin da yake gudanar wa saboda matasa dake da shaawar wadanni inda ake sanya gasa dake bada dama ga kungiyoyi dake yankin masarautar Rimaye da makwaftan su, abin da Alh Yusif Ke cewa Hakan ya kara kyautata dankon zumunci tsakanin matasan da alummar yankin harma da makwaftansu, wajen bunkasar tattalin arziki ta hanyar wasanni maigirma Dan Isa cewa yayi fara gasar cin kofin “Dan Isa” da akayi a shekaru kullum a na masu sanaoi wadanda kanyi amfani da lokacin wasan dan baje hajjarsu tare da samun ciniki a lokutan wasan da ake a garuruwa daban daban,

Da yake karin haske kan yadda gasar zata kara hada kan mutane jihar da jihar kano dake makwaftaka da jihar katsina, Alh Yusuf Yakubu cewa yayi inganta alakace ta sanya gayyatar kungiyoyi daga jihar kano zuwa kasar Rimaye dan shiga gasar kuma yace ko yanzu baka iya rabe dan Rimaye dake katsina da dan tsanyawa wadanda ke makwaftaka da garin saboda kyakykyawar alaka,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *