A yau laraba masarautar Birnin kano ta fidda sanarwar haramta Hawan Kilisa,atisaye da angwanci a fadin yankin masarautar,
Dayake bayani a madadin masarautar Hakimin Dala Lamido Abdullahi Bayero cewa yayi masarautar ta yanke hukuncin hana hawan ne duba da irin abubuwan da hawan ke haifarwa tsakanin mahayan da alumma inda sauda dama akan samu rigingimu. Da fadace fadace,
Ko a baya ansha jin alumma na kokawa kan yadda hawan kilisa ke juyewa fadan Daba har wasu lokuta akan rasa rayuka,
Ko a baya asha fadin cewa an hana hawan amma abin yaci tura, abin jira a gani shine shinko wannan sanarwar zata sha banban da wadanda akayi a baya ?