Sabon salon rikicin tsakanin yan jamiyyar APC a jihar ya kai ga bawa hammata iska abin da yayi sanadiyyar raunata juna inda kawo iyanzi kwantar jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar wadanda suka ji munanan raunuka a rikicin da ya barke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Kwara gado a asibiti.
Suna samun kulawar likitoci a wasu asibitoci da ba a bayyana ba a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara, jaridar This Day ta ruwaito.