Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong ne ya bayyana haka yana mai jaddada muhimmancin daukar kwakkwaran matakin hana daukar makamai ba bisa ka’ida ba.

“Ba na goyon bayan mutane su daukai makami, amma a tattaunawa da bincikenmu, mun gano ba Fulani makiyaya ne kadai ke dauke da AK-47 ba, hatta manoma suna dauke da ita,” inji shi.

Da yake bayanin a shirin ‘Sunrise Daily’ na gidan talabijin na Channels, Lalong wanda shi ne Gwamnan Jihar Filato, ya yi tir da rikicin manoma da makiyaya masu dauke da makami.

“Yanzu muna ganin hadarin barin mutane suna yawon kiwo barkatai. Su kansu makiyayan mafita suke nema kuma idan aka yi musu bayani za so su zauna a wuri daya, su daina daukar makami.

“Don magance lamarin, dole ne a dage wajen dakile kwararar kananan makamai.

“Sauran hanyoyi kamar shirin sauya fasalin kiwo na kasa (NLTP) kuma dole ne a rungume su don raba wadannan mutane da tsohuwar hanyar noma a nuna musu tsarin zamani,” inji shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *