Manchester City tana iya daukar dan wasan Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, a bazara mai zuwa idan damar yin hakan ta taso, a cewar wani babban jami’in kungiyar Omar Berrada. (Manchester Evening News)
Har yanzu Manchester United na son dauko dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Haaland, mai shekara 20, da dan wasan Ingila Jadon Sancho, shi ma mai shekara 20. (ESPN)
Real Madrid ta ce ba za ta dauki dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 27 ba, bayan ya ce babban burinsa shi ne watarana ya murza mata leda. (AS – in Spanish)
Dan wasan Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 29, ya kusa tsawaita zamansa a Manchester City da shekara biyu inda zai rika karbar £300,000 duk mako. (Sun)
Dan wasan da Arsenal ta saya a kan £27m dan kasar Faransa William Saliba, wanda har yanzu bai murza mata leda ba, zai tafi zaman aro a Championship, inda ake sa ran Brentford za ta dauki dan wasan mai shekara 19. (Goal)
Dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 31, zai murza ledarsa ta farko tun bayan komawarsa Tottenham inda za su fafata da West Ham a karshen makon gobe. (Telegraph)
Dan wasan Chelsea da Faransa Olivier Giroud, mai shekara 34, ya ce ya kusa tafiya Serie A a watan Janairu da kuma bazara. (RMC Sport, via Football London)
Aston Villa na shirin biyan harajin da ke kanta inda za ta sayar da wasu ‘yan wasanta a yayin da take son sake yunkurin dauko dan wasan Bournemouth dan kasar Norway Josh King, mai shekara 28, wanda ita ma West Ham ta so dauka. (Football Insider)
Villa ta shirya sayar da dan wasan Netherlands Anwar El Ghazi, mai shekara 25, dan wasan Faransa Frederic Guilbert, mai shekara 25, da kuma dan wasan Ingila Henri Lansbury, mai shekara 29, kafin a rufe kasuwar ‘yan kwallon Ingila ranar 16 ga watan Oktoba. (Football Insider)
Manchester City na sa ran kocinta Pep Guardiola zai tsawaita zamansa amma duk da haka za ta nemi sabon kocin don maye gurbinsa idan ya ce zai yi gaba. (Telegraph)
Dan wasan Sufaniya Dani Ceballos, mai shekara 24, ya ce zai koma Arsenal domin yin zaman aro duk da cewa Real Madrid ta bukace shi ya jira zuwa wata daya. (Marca)