VALENTINE DAY: Abubakar Sale Yakub.
Ranar masoya ta Valentine rana ce da Kiristocin yammacin turai suke gudanar da ita domin girmama wani Kirsita mai suna Saint Valentine, bikin ranar yana da muhimmaci ga al’adu da addinin Turawan , kuma rana ce da masoya suke warwasawa a fadin Duniya.
Wannan dai rana bata samu karbuwa ba a kashen Musulmi duk kuwa da cewa wasu matasan Musulmi da suke da karancin ilimin addinin Islama sukan ara su yafa.
Shi dai Saint Valentine, ya kasan ce mabiyin addinin Kirista wanda ya rika daurawa Sojojin daular Rum aure aboye wanda yin hakan haramune a ga tsarin addinin kiristanci a daular Rum, hakan ne ya ja aka daure Valentine a gidan kurkuku, inda ake tunawa dashi a ranar 14 ga watan Fabrairun ko wacce shekara.
A bisa al’ada Saint Valentine, idonsa ya rufe akan ‘yar shugabansa, wadda ya rubutamata wasika, inda yace Valentine yanai mata bakwana kafin a zatar mas ada hukunci.
Fafa Roma Gelasius na daya, shine mutumin daya sanya ranar 14 ga watan Fabrairun na shekarar 496 a matsayin ranar girmamawa ga Saint Valentine na daular Rum wanda ya mutu a shekarar 269 bayan haihuwar annabi Isa Alaihil salam.
Sai dai fa a yanzu matasan musulumi sun ara sun yafa game da wannan rana w ace aka yaudaresu a matsayin ranar maso wadda bata da wata alaka da addinin Islama.
A wani nazari da gidan Radiyo Express yayi, ya gano cewa dayawa daga cikin al’ummar basu san asalin ranar masoya ta Valentine ba, lamarin dayasa suke zake wajen taya bera bari.
Malam Abubakar Rabo Abdulkareem tsohon shugaban hukumar tace fina finai ta jihar Kano,’’ yace ba dai dai bane matasan musulmi su rika yin murna ga wannan rana domin bata da wata alaka ga musulunci, kuma wasu matasan sukan aikata balada a wasu cibiyoyi da guraren shakatawa a fadin Jihar Kano’’
‘’Ya kuma ja hankalin iyaye dasu ciagba da sanya idanu akan ‘ya yansu domin kaucewa kitso da kwarkwata’’.
Tuni dai Hukumar Hisbah ta Jihar Kano tabakin tace sun sanya kafar wando guda da matasan dake raya wannan rana ta Valentine, wandda aka turowa matasan musulmi a matsayin ranar masoya.
A karni na 14 Geoffrey Chaucer, ya fara mika fulawar soyayya da sunan ranar masoya, haka a karni na 18 a kasar Ingila bikin ya cigaba da habaka ta hanyar gabarawa masoya furanni da katina masu dauke da kalaman soyayya, yayin da a karna na 19 da 20 da 21 wasu na amfani da shafukan sada da zumunta da aikewa da hotuna da sunan nuna kauna ga masoya.
Ranar masoya ta Valentine, babu wata kasa a fadin Duniya dake bin addinin Kirista data ayyana bikin wannan rana a hukumance, balle ace wata kasar al’ummar Musulmi tayi kasadar hakan.
Contact Information
114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano
We Are Available 24/ 7. Call Now.
- 21 September, 2023
Share: