Da alama Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun soma dawowa daga rakiyar Gwamnatin Muhammadu Buhari sakamakon abin da suke cewa rashin mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro da ta addabi musamman Arewacin kasar.
Malamai da dama da BBC ta tattauna da su sun ce dole gwamnatin Shugaba Buhari ta zage damtse don shawo kan matsalar tsaron ƙasar idan ba haka ba Allah zai yi fushi da ita.
Wannan jan kunne na zuwa ne bayan waɗanda ake zargi mayaƙan Boko Haram ne sun kashe aƙalla manoma 43 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Malam Aminu Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin da ke jihar Kano, ya shaida BBC cewa ya zama wajibi Shugaba Buhari ya sauya salo wajen tunkarar matsalar tsaron da ke addabar arewacin ƙasar.
“Muna kira ga shugabannin da su ji tsoron Allah su san cewa zai tambaye su rayukan mutane miliyan 200 da suke rayuwa a Najeriya. Kuma alƙawari suka yi mana cewa za su yi iya yin su su ga cewa sun ɗauki mataki a kan harkar tsaro da harkar noma da kiwo da kuma harkar cin hanci da rashawa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa: “Waɗannan abubuwa guda uku yanzu sun ƙara tabarbarewa sun lalace a wannan kasa” don haka ya zama wajibi a shawo kansu.