Dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba ya ce a halin yanzu yana cikin mawuyacin yanayi a sana’arsa ta kwallon kafa saboda yadda ake sanya shi a tamaula a Old Trafford. (RTL via Goal)
Manchester City za ta bayar da muhimmanci wajen daukar dan wasan gaba a 2021, inda take son daukar dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Haaland, mai shekara 20, da kuma dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23. (90min)
Chelsea ta amince ta sayar a dan wasan Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 26, ga Napoli idan zaman aronsa ya kare a karshen kakar wasa ta bana. (Gazetta Dello Sport via Teamtalk)
Dan wasan AC Milan dan kasar Turkiyya Hakan Calhanoglu, mai shekara 26, zai iya kama hanyarsa ta zuwa Atletico Madrid bayan an samu matasala kan tattaunawar kwangilarsa a kungiyar ta Italiya, ko da yake har yanzu Manchester United na son daukarsa. (Mundo Deportivo)
Dan wasan Chelsea dan kasar Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, na son tafiya Barcelona idan aka bude kasuwar musayar ‘yan kwallo ta watan Janairu bayan ya samu matsala a Stamford Bridge. (Sport via Metro)
Rahotanni na cewa daraktan wasanni na Liverpool Michael Edwards ya yanke shawarar kin dauko dan wasan Napoli mai shekara 29 dan kasar Senegal Kalidou Koulibaly a bazarar nan saboda farashin da aka sanya a kansa. (Daily Star)
Tsohon kocin RB Leipzig Ralf Rangnick ya yi amannar cewa dan wasan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 22, wanda Liverpool take son dauka, zai samu nasara a Bayern Munich. (Goal)
Juventus ta shirya daukar matashin dan wasan Ajax Ryan Gravenberch ko da yake za ta iya fuskantar kalubale daga Barcelona a yunkurin sayen dan wasan mai shekara 18. (Tuttosport – in Italian)
Tsohon dan wasan Aston Villa Kevin Phillips ya yi amannar cewa Dean Smith zai rarrashi dan wasan Chelsea da suka karbo aro Ross Barkley, mai shekara 26, domin ya sanya hannu kan kwangilar dindindin a kungiyar. (Birmingham Mail)