Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari zaurenta domin ya yi mata bayani kan matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.
Ƴan majalisar sun yanke shawarar gayyatar shugaba Buhari ne bayan kisan da aka yi wa wasu manoma fiye da 43 a kauyen Zabarmari na jihar Borno.
Majalisar ta ce akwai bukatar shugaban ya yi bayani a kan abin da ya hana karya-lagon mayakan Boko Haram duk kuwa da irin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a kan jami’an tsaro.
Honourable Satomi Ahmed, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin, ya shaida wa BBC cewa an ɗau wannan mataki ne ganin cewa an sha kiraye-kiraye ga shugaban kan neman sake fasalin harkokin tsaro amma babu shiru ake ji.
Satomi ya bayyanawa bbc yanayin da ake ciki ya tabbatar da cewa dole ana neman gyara, amma a iya sanin majalisa ta rasa dalilan shugaban ƙasa don haka ta bukaci ya bayyana a gabanta.
Majalisar ta ce dole shugaban ya fito ya yi bayyani mai gamsarwa kan irin matakan da ya ke dauka da kuma dalilan gamsuwa da ayyukan hafsoshin tsaron ƙasar da ake gani ya kamata a sake zubin su.
Sannan akwai kuma bukatar sanin ina shugaban ya dosa, domin kashe-kashe da sace-sacen da ake gani ya wuce tunani.
Majalisar ta ce talakawa sun bai wa shugaba Buhari amana don haka ba za su amince su ci gaba da zaman ƴan amashin shata ba, in ji Satomi.
Satomi ya ce ana su ɓangaren akwai gazawa a salon yaƙin da jami’an tsaron ke yi da matsalolin tsaro don haka za su so ji daga baƙin shugaban don sani halin da ake ciki.