Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
Sheik Ibrahim Khalil

Majalisar malamai ta jahar Kano ta ce ya kamata a ce gwamnati ta yi nazari kafin yanke hukuncin dawo da gabatar da sallar Juma’a da ta idi a jahar saboda yiwuwar fargabar yaduwar cutar korona.

Shugaban kungiyar Majalisar malaman a Kano, Mallam Ibrahim Khalil ya shaida wa BBC cewar duk da cewar gwamnatin jahar ba ta tuntube su ba a yayin yanke wannan hukuncin da ta yi, amma ya kamata ace ta yi la’akari da bukatar mutane.

Malaman Ibrahim Khalil, ya ce wajibi ne gwamnati ta kalli damuwar mutane da kuma abin da ya dace ga mutane tun da bata tuntubi majalisar malamai a kan matakin data dauka ba.

Ya ce ” Amma irin wannan yanayi na annoba da ake ciki tun da har an bayar da umarnin zuwa sallar Jumma’a da ta Idi, to duk wanda yake jin tsoron cewar zai kamu da cutar ko kuma zuwa masallacin zai iya zame masa hadari don yana da wata lalura, to zai iya zamansa a gida”.

Amma wanda kuma yake ganin shi zai iya zuwa masallacin ba tare da wata matsala ba, to shi wannan zai iya zuwa masallaci ya yi sallah in ji malamin.
Ya ce ” Batun a rinka cewa duk wanda bai je masallaci ba ya aikata zunubi, to ba haka abin ya ke ba in dai har yana da kwakkwaran dalilin”.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *