Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima saboda annobar korona.

Majalisar ta amince da naira tiriliyan 10.8, sai dai ta sauya ɓangarori da dama, inda suka ƙara yawan kasafin a ma’aikatu ba kamar yadda Buhari ya gabatar musu ba a ƙarshen watan Mayu.
An samu ƙarin naira biliyan biyar (N5,256,207,430) a kan wanda Buhari ya miƙa musu tun farko – yanzu ya zama naira tiriliyan N10,810,800,972,72 maimakon N10,805,544, 664,642.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage yawan kasafin ne sakamakon halin da annobar korona ta jefa tattalin arzikinta.
*Hukumomi da ma’aikatun da sauyin ya shafa:
*Hukumar Tsarin Ilimin Bai-Ɗaya: N816,517,124
*Ma’aikatar Lafiya a Matakin Farko: N897,641,688
*Hukumar Ci Gaban Yankin Arewa Maso Gabas: N816,517,124
*Hukumar Ci Gaban Neja-Dalta: N1,743,411,240