Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta ce tilas Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya bayyana a gabanta don amsa wasu korafe-korafe duk da cewa sarkin bai bayyana ba kamar yadda hukumar ta gayyace shi.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce tuni suka gayawa lauyoyin sarkin cewa ya bayyana a hukumar ranar Litinin, 9 ga wannan watan.
Maimartaba Sarkin Kano, dai yana fuskantar tuhume-tuhume daga bangarorin gwmnati daban-daban ko a jiya Alhamis ma majalisar dokokin jihar ta kaddamar da wani binciken a kan sarkin.
Sai dai kawo yanzu bangaren Sarkin Kanon ba su ce komai ba tukuna.
Barista Muhuyi ya ce sashe na 31 na dokar da ta kafa hukumar ya tanadi duk wanda aka gayyata ya zo da kansa.
Daga nan ne sai shugaban hukumar ya ce idan bayan cikar wa’adin ranar Litinin ba a samu yin hakan ba, “to ka’idojin da doka ta tanada shi za a yi.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *