
Mahaifiyar kocin Manchester City, Pep Guardiola ta mutu bayan kamuwa da cutar coronavirus tana da shekaru 82 da haihuwa.TALLA
Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta bayyaana kaduwarta da mutuwar Dolors Sala Carrio a garin Manresa na birnin Barcelona da ke Spain.
Tuni masu alaka da Manchester City suka yi ta mika sakwannin ta’aziya ga Guardiola da danginsa da abokan arziki.
Mutuwar mahaifiyar Guardiola na zuwa ne a daidai lokacin da Spain ta sanar da samun raguwar mamatan da coronavirus ke kashewa a kullum, inda a wannan Litinin cutar ta kashe mutane 637, adadi mafi kankanta cikin kwanaki 13.