Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar kwallon kafa ta Lyon ta yi waje da Manchester City a Gasar Zakarun Turai da aka buga a daren Asabar a birnin Lisbon na kasar Portugal.

Yawancin masu nazarin kwallon kafa Manchester City suka ba nasara gabanin a fara wasan, amma ƴan wasan Lyon sun kasance ba kanwar lasa suke ba a wasan da ya ƙayatar matuƙa.

Lyon ce ta fara zura kwallo a ragar City a minti na 24 bayan da Maxwell Cornet ya karɓi wata ƙwallo kuma ya aika ta cikin raga.

Amma a minti na 69 Kevin de Bruyne ya farke kwallon bayan da Raheem Sterling ya yi ma sa wani kyakkyawan kuros.

Sai dai Lyon ta shigar da ɗan wasanta Moussa Dembele – wanda tsohon dan wasan ƙungiyar Celtic ta Scotland ne – kuma ya ci wa Lyon ƙwallo ta biyu ana minti 11 a tashi wasan.

Wani abin mamaki da ya faru shi ne na wata kwallo da Raheem Sterling ya barar bayan da Gabriel Jesus ya damka ma sa ita a gaban mai tsaron gidan Lyon amma sai ya buga ta sama.

Kuma ana sake fara wasa sai Moussa Dembele ya ci kwallonsa ta biyu wadda ta zama kwallon Lyon ta uku ke nan.

Bayan wannan wasan na yau, an kammala dukkan wasannin kusa da na daf da na ƙarshe ke nan, kuma Lyon za ta kara da Bayern Munich a matakin daf da na ƙarshe ranar Laraba mai zuwa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *