
Hukumar dake shirya gasar Firemiyar Najeriya zata yanke hukunci kan ci gaban gasar ta bana 2019/2020 ko dakatar da ita bayan buga wasan mako 25 ranar Laraba
Wannan ya biyo bayan matakan da hukumomin lafiya ke dauka kan cutar Coronavirus wanda tasa dakatar da manyan wasannin a wasu sassa na duniya ko yi wasan ba tare da yan kallo ba.
Tuni dai aka dakatar da gasar Firimiyar Ingila, La Liga a kasar spain da bundesliga da kuma Serie A ta kasar Italia inda cutar tafi kamari a turai, inda a safiyar Talata, aka dakatar da Wasannin guje guje da tsalle tsalle na kasa da za ayi a Benin dake jihar Edo a ranar 22 ga Maris.
Shugaban Shugaban Hukumar LMC shehu Dikko ya bayyana cewa a ranar Talata za a yi wani taro bayan wasan na mako na 25 da zaayi Laraba don sanin ko ya kamata a ci gaba da gasar ko kuma a buga shi batare da yan kallo ba.
“Game da batun COVID 19, dikko cewa yayi yazama dole mu sa ido tare da bin umarnin gwamnati kuma mu kasance muna yin tambayoyi ta bakin Ministan Wasanni da tuntuɓar hukumomin kiwon lafiya,
“Saboda haka bayan wasannin NPFL gobe, dole ne mu sake dubawa idan har za a mayar da dukkanin wasannin gida batare da yan kallo ba kamar yadda ake yi a wasu kasashe kamar Turkiyya ko kuma jinkirta gasar zuwa makwanni.
Dikko ya kara da cewa, “Zamu kuma ci gaba da aiki tare da kungiyoyin don kafa hanyoyin yin rigakafi, da daukar matakan kariya a duk wuraren wasannin da suka hada da wayar da kan jama’a kamar yadda hukumomin lafiya suka shawarce su,” in ji Dikko.
Za a buga wasan mako 25 na gasar Kwallon Kwararru ta Najeriya a ranar Laraba, 18 ga Maris tare da wasanni 10 a cibiyoyin wasannin.