Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga -Salisu M.Jegus

Da kyar da gumin goshi Liverpool ta doke West Ham United a karshen wasan mako na 27 a gasar Premier da suka kara a Anfield.
Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Georginio Wijnaldum a minti na tara da fara wasa, sai dai kuma minti uku tsakanin Issa Diop ya farke wa West Ham kwallo.
Bayan sun sha ruwa sun koma fili ne West Ham ta kara na biyu ta hannun Pablo Fornals, hakan ya tashi hankalin ‘yan kallo.
Daga nan ne Liverpool ta saka kai mi ta farke ta hannun Mohamed Salah daga baya kuma Sadio Mane ya kara na uku saura minti tara a tashi wasan.

Liverpool ta ci wasa 21 a jere a gida a gasar Premier, karo na biyu kenan tana haka, bayan bajintar da ta yi tsakanin Janairu zuwa Disambar 1972 karkashin Bill Shankly.
Da wannan sakamakon Liverpool na nan a matakinta na daya a kan teburi da tazarar maki 22 tsakaninta da Manchester City ta biyu.
West Ham kuwa tana nan ta 18 cikin ‘yan kasan teburi da maki 24.
Liverpool za ta ziyarci Watford a wasan mako na 28 ranar 29 ga watan Fabrairu, ita kuwa West Ham za ta karbi bakuncin Southampton a ranar ta Asabar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *