Bai zama abin mamaki ba irin goyon bayan da Bola Ahmad Tinubu ya Samu ba daga Malamai Addini da Limaman Juma’a a Jihar Kano ba, duba da irin tasirin da addini keyi a siyasar Najeriya,
Bala Ahmad Tinubu yaje jihar kano dan halartar bikin Daurin Aure a Mina Event inda zuwan nasa ya rikide zuwa taron ganawa da kulle kullen siyasa ganin yadda shekara ta 2023 ta tunkaro .
Bayan Kammala taron ne Jagoran APC ya wuce zuwa masallachin Alfurqan da ganawa da Babban limamin Masallacin Dr Bashir Omar inda kuma ya hadu da Dr.Ahmad Datti wanda Tinubun ya ambaceshi da cewa tsohon abokinsa ne inda sukayi wata ganawar sirri ta Kimanin Mintina 10,
Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa bayan kammala taron Alfurqan ne JAGABAN ya wuce zuwa Chalawa Phase 2 inda Malaman Kano da Suka Hadar da Tijjaniyya, Kadiriyya da Izala suka hadu dan ganawa dashi inda jagoran Tijjaniyya Shehi Shehi Maihula daga Darikar Tijjaniyya da yayi Jawabi a Madadin Su yace ya zana wajibi ga yan arewa su ramawa kura aniyarta duba da yadda Bola Ahmad Tinubu ya jajirce wajen tabbatar da samun nasarar shugaba Buhari a lokacin da Buharin yayi ta faduwa kafin Samun Tallafi daga Tinubu a Shekara ta 2015, abin da wakilin Tijjaniyyar yace Baza a manta ba,