Majalisar dattawa ta mika goron gayyata ga ministan tsaro da shugabannin tsaro bayan satar daliban makarantar GSSS Kankara.
Gwamnatin Matawalle ta kulle makarantun Zamfara dake makwabtaka da Katsina da Sokoto.
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar shirin hukumar NDE na daukar ma’aikata na musamman guda 774,000.
Gwamnatin tarayya ta samar da kwamitin da zai dinga kulawa da farashin man fetur.
Shugaban ‘yan sandan Najeriya, Adamu Muhammad ya bayar da umurnin rarraba jami’an SWAT.
An rantsar da Hamisu Chidari sabon Shugaban Majalisar dokokin Kano bayan tsohon shugaban ya yi murabus.
Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin cewa su suka sace daliban makaerantar Kankara da ke jihar Katsina.
Covid-19: Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a, Tanko Muhammad ya kamu da cutar.
Yajin aikin ASUU: Ministan kwadago da ayyukan yi, ya tabbatar da tsarin nan na babu-aiki babu-biya.
Tsohon Gwamnan Abia, Sanata Orji Kalu y ace zamansa a gidan yari ya sanya shi zama mutumin kirki.
Gwamantin jihar Lagos za ta fara sayar da buhun shinkafa a kan Naira 20,000.
Mutane 14 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa dauke da ‘yan gudun hijira a gabar tekun Venezuela.