Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 242 a Najeriya a 2020.
Rundunar Sojoji sun tarwatsa mafakar Boko Haram, sun yi raga-raga da Sambisa.
Shugaban hukumar NPA, Hadiza Bala Usman ta ce, alkaluma na mizanin tattalin arziki (GDP) zai bunkasa idan aka zuba dimbin jari a tashoshin jiragen ruwa.
Ƴan bindiga sun hallaka Alhaji Audu, dillalin shanu a Jihar Zamfara saboda ya ƙi siyan shanun sata.
Wata babban kotu da ke Ringim jihar Jigawa ta yankewa wani matashi mai musa Mustapha hukunci kisa ta hanyar rataya bayan ya kashe budurwarsa.
COVID-19: Shugaban hukiumar NCDC ya gargadi ‘yan Najeriya da su rika kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka shimfiɗa domin a watan Janairu cutar za ta kara munana.
Mahara sun yi garkuwa da da wasu matan aure 2 a Gwagwalada, Abuja.
2021 UTME: Hukumar JAMB ta karyata rahoton sayar da fom din jarabawar.
Najeriya ta ƙwace fasfon matafiya 100 saboda sun ƙi maimaita gwajin korona.
Wani harin bom ya hallaka mutum 12 filin jirgin Yemen.
COVID-19: Jamhoriyar Nijar za ta fara allurar rigakafin cutar Corona a sabuwar shekara ta 2021.
Wani zababben dan majalisa a Amurka mai suna Luke Letlow ya rasu sakamakon cutar Covid-19 tun kafin a rantsar da shi a majalisa.