Majalisar wakilai ta janye gayyatar Buhari, ta nemi afuwarsa.
Babban Bankin Najeriya, CBN ya ce darajar Naira za ta kara faduwa a shekarar 2021.
Boko Haram ta kashe masu faskare uku, ta kama 40 a Borno.
Ministar Harkokin Mata ta Najeriya Dame Pauline Tallen ta kamu da cutar Corona.
‘Yan bindiga sun kashe jigon jam’iyyar PDP a karamar hukumar Bosso da ke jihar Niger, Alhaji Ahmodu Mohammed tare mutane 3.
Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya musanta rade-radin da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.
Gwamnati ta nemi Bishop Kukah ya daina ruruta wutar rikici da kiyayya a Najeriya.
‘Yan bindiga sun sace mutane 48 a daren Asabar a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Sojoji sun kashe masu iƙirarin jihadi 12 a Mali.
Covid-19: Bill Gates ya ce sun gaza gano dalilan da suka hana coronavirus tafka barna a Afrika.
Al’umman Jamhoriyar Nijer na cigaba da kada kuri’ar zaben sabon shugaban kasa da ‘yan majalisun kasar a yau.
An yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda a Siriya.
EPL: Leeds United ta sami nasara a kan Burnley da ci 1:0 a wasan da suka buga yau.