Majalisar dattijai ta ce akwai bukatar shugaba Buhari ya sake duba umarnin da ya bayar na tsige Nasiru Argungu daga mukaminsa.
Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce Malaman addini na matukar kawo masu tsaiko wajen yaki da cutar Corona.
Cutar korona ta hana Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, zuwa ɗaurin auren ɗansa Hamisu.
Jam’iyyar PDP ta ce Shugaba Buhari tsoro ne ya hana shi bayyana a gaban majalisa kan rashin tsaro.
‘Yan sandan Kaduna sun musanta kashe mutum 16 da ‘yan bindiga suka yi a jihar.
Hukumar EFCC a jihar Lagos sun kama wani likitan bogi da ya yi zambar Naira milyan 10.
Gwamnatin Najeriya ta shirya karbar riga-kafin mutum miliyan 20.
Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Mai Shari’a Sylvanus Adiewere Nsofor ya rasu.
Majalisar wakilai a Argentina ta amince da halarta zubar da ciki a kasar.
Tarayyar Turai ta amince da rage yawan gurɓataccen iska nan da 2030.
An kwace muggan makamai daga hannun ‘yan ta’adda a arewacin Iraki.