An sami karin mutane 397 da suka kamu da Coronavirus a Najeriya jimilla 98,811.
Gwamnatin tarayya ta umurci jami’o’i su dakatar da batun sake buɗe makarantu har sai an ga yanayin Corona tukuna.
‘Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a jihar Katsina, sun sace mutum 50 harda sabbin aure.
Mafusata sun kona wasu mutane 2 da make zargin ‘yan fashi da makami ne a Ibadan.
Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto zai sauya kwalejin Ilimi ta jihar zuwa jami’a.
Jami’an tsaron Algeria sun kame yuro dubu 80 da ake shirin mikawa ‘yan ta’adda.
COVID-19: Shugaba Ramaphosa an Afrika ta Kudu ya haramta sayar da giya a kasar.
Sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sama da 100 na neman mafaka a Kamaru.
An kashe ma’aikatan gwamnati 2 a wani hari da aka kai Gazne da ke Afganistan.
Isra’ila ta bayar da umarnin kar a yi allurar riga-kafin Corona ga Falasdinawan da ta tsare.
EPL: Crystal Palace da Leicester City sun tashi 1:1 a wasan jiya.