An sami karin mutane 501 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 78,434.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 3 da yin garkuwa da mai gari a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Sojoji sun ce sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da kama daya a Katsina-ala ta jihar Benue.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce Najeriya ta shiga mawuyacin hali ne a lokacin Covid-19 sakamakon rashin daukar shawararsu.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi tsinuwa ga duk mai hannu wajen sake sanya dokar kulle.
Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Habu Galadima shugaban cibiyar NIPSS.
Gwamna Zulum na jihar Borno ya bai wa matsakaitar ‘yan kasuwa 704 tallafin Naira milyan 32.
Hukumomin Kamaru sun ce ‘yan kasuwa da ‘yan siyasar kasar na hulda da Boko Haram.
Hukumar da ke lura da lafiyar jiragen sama ta Turai ta tabbatar da lafiyar jirgin Boeing samfurin 737 Max.
Hukumar Cyber Security ta kasar Amurka ta ja kunnen cewa satar bayanai ta yanar gizo ka iya karuwa a Amurka da fadin duniya.
EPL: Manchester United ta sami nasara a kan Leeds United da ci 6:2 a wasan jiya.
EPL: Aston Villa ta sami nasara a kan West Bromwich Albion da ci 3:0 a wasan jiya.
LaLiga: Real Madrid ta sami nasara a kan Eibar da ci 3:1 a wasan jiya.