An sami karin mutane 418 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 73,175.
Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya killace kansa saboda tunanin ya harbu da Coronavirus.
Manyan sojojin Najeriya 18 sun kamu da cutar Coronavirus.
Ministan tsaro, Janar Magashi ya ce nan ba dadewa ba za a gano daliban da aka sace a Katsina.
Hukumar Kwastom a yankin Yauri ta jihar Kebbi sun yi nasarar cafke wata mota dankare da harsashi da bibdigogi da aka yo safararsu daga Nijar.
Gwamna Ganduje zai gina wa malamai gidaje dubu biyar 5,000 a jihar Kano.
Gwamnatin Najeriya ta ce an yi wa ƴan bindiga da suka sace ɗalibai ƙawanya a Kankara.
Ƙungiyar Boko Haram ta kai hari a yankin Diffa na Nijar inda ta kashe aƙalla mutum 27.
Gwamnatin Eswatini ta sanar da mutuwar Firaiminista Ambrose Dlamini, mako hudu bayan kamuwa da cutar korona.
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce Isco ba ya cikin wadanda ya ke son yin aiki da su nan gaba.
LaLiga: Barcelona ta sami nasara a kan Levente da ci 1:0 a wasan jiya.
EPL: Liverpool da Fulham sun tashi 1:1 a wasan jiya.
EPL: Burnley ta sami nasara a kan Arsenal da ci 1:0 a wasan jiya.