An sami karin mutane 749 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 85,560.
Shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta shawo kan tsadar abinci a shekara mai zuwa.
Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 6 a Katsina.
Gwamnatin jihar Benue ta haramta amfani da babura a kananan hukumomin Katsina-ala da Ukum a jihar.
Jami’an tsaro sun kashe ɓarayin shanu 9 hanyar Kaduna-Abuja.
Shugaban Jam’iyyar Labour (Labour Party) na Kasa, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ya rasu.
Mutum 5 suka rasa rayukansu a girgizar kasa da ta auku a Croatia.
Za a yi muhawara kan amincewa da kudurin halarta zubar da ciki a Argentina.
An yankewa ‘yan ta’adda 168 daurin rai da rai a kasar Egypt.
EPL: Manchester United ta sami nasara a kan Wolverhampton da ci 1:0 a wasan jiya.
EPL: Arsenal ta sami nasara a kan Brighton da ci 1:0 a wasan jiya.
LaLiga: Barcelona da Eibar sun tashi 1:1 a wasan jiya.
LaLiga: Sevilla ta sami nasara a kan Villarreal da ci 2:0 a wasan jiya.