An sami karin mutane 829 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 83,576.
Buhari ya yi ta’aziyyar likitoci 20 da Corona ta kashe a cikin mako guda.
Yan bindiga a Kaduna, sun sace wani Fasto, Emmanuel Egoh Bako tare da matarsa Cindy Bako.
Wani bangaren jam’iyyar APC a Jigawa ya zargi Gwamna Badaru da kokarin rusa jam’iyyar.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta kaddamar da jiragen yaki nasu saukar ungulu.
Hukumar CIPC ta bankado rashawa a ma’aikatar shara’ar Najeriya na Naira bilyan 9.4
Ana tsare da wani mai shirya fina-finai a Bangladesh bisa zargin nuna wani bidiyo.
Covid-19: Faransa ta karbi alluran farko na Pfizer da BioNTech.
An kashe mutum 8 yayin bikin Kirsimeti a Colombia.
Hukumar FIFA ta soke wasannin cin kofin kwallon kafa na yan kasa da shekaru 17 da -20.
EPL: Arsenal ta sami nasara a kan Chelsea da ci 3:1 a wasan jiya.
EPL: Manchester City ta sami nasara a kan Newcastle United da ci 2:0 a wasan jiya.