Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An sami karin mutane 675 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya jimilla 71,344.

Gwamnatin jihar Osun ta roki Gwamantin tarayya ta taimaka wajen gina filin sauka da tashin jiragen sama a jihar.

Gwamna Ganduje na jihar Kano ya jajantawa iyalan mutane 16 ‘yan asalin jihar da ‘yan bindiga suka kashe a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Jami’ar jihar Lagos ta kara kudin makaranta da kashi 168% ga sababbin dalibai.

‘Yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP sun nemi Buhari ya yi watsi da maganar Malami ya amsa gayyatar su.

Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya su ne mafi nagarta a cikin Afirka.

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da dan majalisa a jihar Taraba sun bukaci miliyan 150, a matsayin kudin fansa.

Gwamnatin Ingila ta dakatar da Tsohon shugaban kasar Gambia, Jemme da matarsa shiga kasar tare da kwace kaddarorinsu da ke kasar.

Shugaba Donald Trump ya aminta da zartar da hukuncin kisa kan bakar fata, Brandon Bernard.

Dan takarar jam’iyyar adawa a Ghana, John Mahama ya yi watsi da sakamakon zaben da aka kammala.

EUROPA: Arsenal ta sami nasara a kan Dundalk da ci 4:2 a wasan jiya.

EUROPA: AC Milan ta sami nasara a kan Sparta Prague da ci 1:0 a wasan jiya.

EUROPA: Napoli da Real Sociedad sun tashi 1:1 a wasan jiya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *