An sami karin mutane 1,867 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 107,345.
Kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 14 a jihar Benue.
Sojojin Najeriya sun ce ya zuwa yanzu babu sauran garin da ke hannun Boko Haram.
Gwamna Wike na jihar Rivers ya yi kira ga Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaro.
Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kawo gagarumin ci gaba a harkar tsaron kasar cikin shekarar nan.
Wani mammunar hatsarin mota ya yi ajalin mutum 14 a jihar Kogi.
Za a yi wa mutane milyan 6 rigafin zazzabi a jihar Bauchi.
Badakalar NDDC: Malami ya karyata amsar Naira bilyan 25 daga hannun Akpabio.
Makarantar koyon aikin lauyoyi na Najeriya ta ki amsar daliban da suka yi karatu a Jamhoriyar Benin.
Gwamnatin Netherland ta sauka kan baɗaƙalar damfara dagane da walwalar yara.
Mutane 35 sun rasa rayukansu sakamakon afkuwar girgizar kasa a Tsibirin Sulawesi na kasar Indonesiya.
Shugaba Museveni na kasar Uganda na kan gaba a kuri’un da ake kirgawa.