Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An sami karin mutane 1,074 da suka kamu da cutar Corona a Najeriya, jimilla 88,587.

Jam’iyyar PDP ta ce babu komai a cikin jawabin Buhari na sabuwar shekara sai hauma-hauma da soki-burutsu.

Sojoji sun ce, sun sami nasarar kashe ‘yan bindiga a Jihohin Zamfara da Katsina tare da ceto mutum 10.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ce Buhari ya fi sha’awar karantawa ‘yan Najeriya jawabi fiye da aiki.

’Yan gudun hijira 800,000 ne a sansanoni ke nukatar tallafin abinci, a cewar Gwamna Zulum na jihar Borno.

Gwamnatin Jihar Osun ta ce ba za ta bude makarantu ranar 4 ga watan Janairun 2021 ba, sabanin sanarwar da ta bayar tun da farko.

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto ya sauke shugabannin kwamitin riko na kananan hukumomi 23 a jihar.

Hukumar UNICEF ta yi harsashen cewa a Najeriya an haifi jarirai sama da dubu 21 a ranar sabuwar shekara.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da Iran kan hukuncin kisan wani matashi.

Mata za su fara tuƙin jirgin ƙasa da gyaran mota a Rasha.

Ingila ta kammala ficewa daga Tarayyar Turai bayan kusan shekara 50 a matsayin memba.

Iran na shirin ƙara inganta sinadarin uranium ɗinta zuwa kashi 20 cikin 100.

EPL: Manchester United ta sami nasara a kan Aston Villa da ci 2:1 a wasan jiya.

EPL: West Ham United ta sami nasara a kan Everton 1:0 a wasan jiya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *